Shehu Sani ya Karyata Maganar da Aka Fada Akan Gowon

 

Sanata Shehu Sani ya karyata ikirarin da dan majalisar Burtaniya, Tom Tugendhat ya yi na alakanta Yakubu Gowon da wawushe kudin Najeriya.

Tugendhat yayin jawabi a majalisar Burtaniya ya yi ikirarin cewa tsohon Shugaban kasa na mulkin Soja Yakubu Gowon ya kashe kudi kimanin rabin na CBN da zai sauka daga mulki.

Sanata Shehu Sani ya karyata hakan inda ya ce babu alamar Gowon na da irin wannan arzikin tun daga saukarsa da mulki har zuwa yanzu kimanin shekaru 40.

Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya yi wa ɗan majalisar Burtaniya, Tom Tugendhat’s martani kan iƙirarin da ya yi na cewa tsohon shugaban mulkin soja Yakubu Gowon ya bar mulki da kuɗin da kai rabin abinda babban banki CBN ta mallaka.

Tugendhat ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan muhawarar yiwuwar hukunta gwamnatin Najeriya kan zargin keta harkokin bil adama yayin zanga zangar #EndSARS.

Shehu Sani ya ce wannan maganar ba gaskiya bane , inda ya ce Gowon ya sauka daga mulki ba tare da alamun ya tara arziki ba kuma ya cigaba da kasance a hakan fiye da shekaru 40 bayan saukarsa daga mulki.

Shehu Sani ya yi wannan martanin ne ta shafinsa na Twitter a ranar Talata 24 ga watan Nuwamba.

Ga abinda ya rubuta:

“Janar Yakubu Gowon; Iƙirarin ‘sata a CBN’ ta ministan Afirka na ƙasar Birtaniya wadda Mista James Duddridge ya yi game da Janar Gowon ba komai bane illa tsantsagwaron ƙarya.

Gowon ya sauka daga mulki ba tare da alamun yana da arziki ba kuma ya cigaba da zama a hakan fiye da shekaru 40.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here