Shugaban Ma’aikata da Kwamishinoni 4 na Jahar Benue Sun yi Murabus

 

Shugaban ma’aikata na gwamnatin jahar Benuwai, Orbunde, tare da kwamishinoni 4 sun mika takardar murabus.

Kusoshin gwamnatin gwamna Ortom, sun bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne domin samun damar fuskantar siyasar 2023.

Wannan matakin nasu ya zo ne bayan umarnin gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, cewa duk mai son fara siyasar 2023 ya aje muƙaminsa

Benue – Shugaban ma’aikata na gwamnan Benuwai, Fasto Terwase Orbunde, tare da wasu kwamishinoni huɗu sun miƙa takardar murabus domin samun damar fuskantar siyasar 2023.

Kwamishinonin hudu sun haɗa da, kwamishinan yaɗa labarai, Mrs Ngunan Addingi, da kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa, Dondo Ahire.

Sauran sune kwamishinan ilimi, Farfesa Dennis Ityayvar, da kuma kwamishinan matasa da wasanni, kwamaret Ojemba Ojotu, kamar yadda dailytrust ta rawaito.

Wane muƙami suke nema a 2023?

Tsohon shugaban ma’aikata, Orbunde, tsohon kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa da kuma tsohon kwamishinan Ilimi, kowannen su na fatan ya gaji gwamnan jahar, Samuel Ortom.

Yayin da tsohuwar kwamishinan yaɗa labarai, Addingi, da takwaranta tsohon kwamishinan matasa da wasanni, Ojutu, na shirye-shiryen taka takarar yan majlisar wajilai a mazaɓunsu.

Tsafofin makusantan gwamnan Benuwai, sun tabbatar da murabus ɗin su ga manema labarai a Makurɗi, babban birnin jahar.

Na gama aikina, zan tunkari gaba – Orbunde

A wani jawabi da tsohon shugaban ma’aikata, Orbunde, ya fitar, ya bayyana cewa ya kammala aikin da ya kudiri yi, yanzun kuma zai fuskanci aiki na gaba a matsayin gwamna Idan Allah ya so.

Yace:

“Mun fara wannan tafiyar ne tun a shekarar 1995, lokacin da gwamnan Ortom ya nemi na zo mu yi gwagwarmayar yaƙin neman zaɓen Gwamna.”

“Kuma tun wancan lokaci muke aiki tuƙuru har mafarkinmu ya zama gaskiya a shekarar 2015.”

“Duk da an samu matsaloli a tafiyar amma Allah ta hanyar mutanen jahar Benuwai ya baiwa uban gidan na nasara a 2015 da kuma 2019.Kuma na kasance cikin gwamnati na tsawon zangon biyu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here