Datse Asusun Bankinsa: Soja ya Shigar da Karar Rundunar Sojojin Najeriya Gaban Kotu
Wani soja ya shigar da rundunar sojojin Najeriya a kotu bisa daskarar da asusun bankinsa.
Ya nemi kotu ta ba rundunar sojoji da wani banki umarnin dawo masa da kudadensa.
Ya kuma nemi kotu ta hana bankin da rundunar sojoji taba kudadensa da daskarar da asusunsa.
Abuja – Wani Manjo a rundunar sojoji, Akeem Adeeogba Osenifor ya maka sojojin Najeriya da bankin FCMB kan wasu kudade.
Manjon ya zargi rundunar sojoji da bankin da daskarar da asusun bankinsa tare da binciken gidansa ba tare da umurnin kotu ba, SaharaReporters ta rawaito.
Read Also:
A cikin karar da ya shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, jami’in ya roki kotun da ta umarci wadanda ake kara su biya shi wasu makudan kudade da suka kai N16.6m a matsayin kudin da yake zargi an sace daga gidansa tare da wasu kadarori masu daraja.
Lauyan sa, Mike Ozekhome, SAN ya gabatar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1104/2021 da ke neman a bi masa kadunsa kan take hakkinsa da aka yi.
Mai shigar da karar ya kuma ce yana son kotu ta umarci Sojojin Najeriya da su cire ‘Post No Debit’ (PND) da aka sanya a asusun sa da kuma umartar tilas ga FCMB ta nemi afuwar sa a cikin akalla jaridu uku na kasa saboda cin zarafin da aka yi masa ba tare da bin tsarin doka ba.
Ya nemi a ba da umarnin hana wadanda ake kara, wakilan su, ma’aikatan su, masu binciken su, da sauran masu ruwa da tsaki kan cire shi a PND ba tare da ingantaccen umarnin kotu ba.