Shugaba Tinubu ya ƙara wa Babban Sufeton ‘Yan Sanda Wa’adin Shekara 3

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarawa Babban Sefotun ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun, kamar yadda wata majiya daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta bayyana.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito an ƙara wa shugaban ‘yan sandan wa’adin shekara uku ne, ma’ana sai zuwa 2027.

Ta ruwaito cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume ne ya bai wa Babbab Sufeton ‘yan sandan takartar ƙara masa wa’adin a ranar Litinin.

A watan Yulin da ya gabata ne Majalisar Dattijan Najeriya ta yi garambawul ga dokar ‘yan sanda ta 2020 ƙarƙashin sashe na 8, wadda ta ci karo da ƙarawa ma’aikacin gwamnati wa’adin aiki bayan shekara 35 ko kuma bayan kaiwa shekara 60 a raye.

Egbetokun wanda aka naɗa IG a watan Yunin 2023 zai cika shekara 60 ne a gobe 4 ga watan Satumba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here