An Tsinci Gawar Faston da Aka Sace a Jihar Edo

 

An tsinci gawar wani fasto na cocin Katolika a jihar Edo da ke kudancin Najeriya, bayan sa’o’i da sace shi.

Wani daga cikin shugabannin cocin, ya ce an sace Father Christopher Odia ne daga gidansa a Ikabigbo, ranar Lahadi a lokacin da yake shirin tafiya cocin domin ibada.

Shedu sun ce mutanen yankin nasu ne da sauran jami’an tsaro da suka bazama nema cikin fushi suka gano gawar.

Lamarin ya faru ne kasa da sa’a 24 da kashe wani limamin coci, Father Vitus Borogo, a gonarsa a yankin kudu maso yammacin Najeriya, kuma mako uku bayan da wasu ‘yan bindiga suka kashe masu bauta a coci akalla 40 a jihar Ondo.

Najeriya na fama da gagarumar matsalar tsaro, inda ake fama da satar jama’a domin karbar kudin fansa da kisan gilla a sassan kasar daban-daban.

A kan hakan ne ma gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar ta shawarci jama’a da su mallaki makamai domin kare kansu daga barayin daji masu satar jama’a da ke addabarsu, kiran da ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin kasar a halin yanzu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here