Ƴan Bindiga Sun Buɗe wa Ƴan Makarantar Islamiyya Wuta Tare da Kashe Likita a Zamfara

 

Wasu ƴan bindiga sun kai hari kan garin Jangebe da ke Ƙaramar Hukumar Talatar Mafara a jihar Zamfara, inda bayanai suka ce sun kashe mutane tare da yin garkuwa da wasu.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu shi ne wani sanannen likita, sannan kuma ƴan bindigar sun yi garkuwa da yariman garin.

Dan uwan likitan wanda ya zanta da BBC, ya ce ƴan bindigan sun je gidan likitan ne da misalin ƙarfe 12 na dare.

Ya ce “suna zuwa gidan sai suka harbe shi, harbi huɗu suka yi mashi.”

Ya kuma ce ƴan bindigan sun tafi da matan marigayin biyu da yara huɗu.

Baya ga wannan, a yankin Shinkafi kuma ƴan bindiga sun buɗe wa wasu daliban makarantar Islamiya wuta.

Hon Aliyu Moyi wanda ya tabbatar da faruwar hakan ga BBC, ya ce ƴan bindigan sun tafi da wasu daga cikin ɗaliban, sai dai babu wanda ya rasa ransa a cikinsu.

Rundunar ƴan sanda reshen jihar Zamfara dai ba ta ce komai ba kan batun duk da cewa BBC ta yi ƙoƙarin tuntuɓarta ta hanyar kiran mai magana da yawunta ta waya.

A yanzu haka dai mazauna wasu kananan hukumomin jihar Zamfara na kokawa dangane da yadda ‘yan bindiga ke kai musu jerin hare-hare, waɗanda ke sanadiyyar rasa rayuka da dama, da kuma garkuwa da wasu domin neman kuɗin fansa.

Hakan na zuwa ne a lokacin da damina ta faɗi a yankin, inda akasarin mazauna suka kasance manoma.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here