‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Jahar Kebbi Sun Tafi da Shanu 500

Yan bindiga sun kai hari wasu garuruwa a karamar hukumar Sakaba na jahar Kebbi.

Yan bindigan da suka shiga garin kan babura sun sace kimanin shanu 500 a cewar shugaban yan banga.

Ba a rasa rai ba yayin harin na yan bindigan domin shanu kawai suka zo Yan bindiga, a ranar Lahadi, sun sace shanu 5000 a garuruwa daban-daban a karamar hukumar Sakaba a jahar Kebbi, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar yan sakai na masarautar Zuru, John Mani, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin magana da majiyar Legit.ng a hirar wayar tarho.

Ya ce hatsabiban yan bindigan sun dade suna adabar mutanen masarautar a cikin yan makonnin baya bayan nan.

Sakaba na daya daga cikin kananan hukumomi hudu da ke masarautar Zuru a jahar ta Kebbi.

A ranar alhamis da ta gabata, yan bindiga sun halaka mutane 88 a kauyuka takwas a kananan hukumomin Danko/Wasagu.

A cewarsa, yan bindigan da suka saba kutsawa garin ta cikin jahohin Kebbi/Zamfara da iyakokin Kebbi/Niger sun kai hari a garuruwan da tsakar rana sun sace shanu da dama.

Mani ya ce babu wanda ya rasa ransa a garin sakamakon harin yan bindigan da suka zo da babura kimanin 500, kowanne dauke da fasinja daya ko biyu.

Ya ce, “Yan bindiga daga Zamfara da Niger sun kai hari wasu garuruwa a karamar hukumar Sakaba na jahar Kebbi sun sace shanu a ruga biyar.

“A kowanne ruga, akwai a kalla shanu 500. Ba su kashe kowa ba duba da cewa shanu kawai suka zo sata.”

Mai magana da yawun yan sandan jahar, DSP Nafiu Abubakar, bai dauka wayarsa ba da wakilin majiyar Legit.ng ya kira shi domin jin ba’asi.

Bai kuma amnsa sakon kar ta kwana da aka aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here