‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaro 19 a Jahar Kebbi

Kebbi- Yan bindiga sun sake kashe jami’an tsaro 19 cikinsu akwai sojoji 13, a jihar Kebbi, a cewar wata majiyar tsaro da mazauna gari a ranar Laraba, rahoton The Punch.

An yi artabun ne a daren ranar Talata a kauyen Kanya da ke Danko-Wasagu, kwana guda bayan an kashe dimbin yan sakai a yankin.

Daruruwan yan bindiga sun afka Kanya, inda suka fafata da sojoji da yan sanda na tsawon awa uku a cewar majiya da kuma mazauna garin.

“Yanzu mutane 19 aka tabbatar da mutuwarsu. Sun hada da sojoji 13, yan sanda biyar da dan vigilante daya, ” a cewar majiyar tsaro da baya so a ambaci sunansa, ya shaida wa AFP.

Ya ce wasu jami’an tsaron ciki har da sojoji guda hudu suna kwance a asibiti ana musu magani saboda rauni da suka yi.

“An gwabza fada sosai na tsawon awanni fiye da uku. Yan ta’addan sun yi galaba saboda suna da matukar yawa.”

Rundunar sojoji da yan sanda ba su yi tsokaci kan lamarin ba da aka tuntube su har zuwa lokacin wallafa wannan labarin.

Muna kyautata zaton yan bindigan da suka kashe yan sakia 57 ne suka kawo mana hari, Arzika

Wani mazaunin garin da ya ce sunansa Musa Arzika, wanda shima ya tabbatar da adadin ya ce maharan sun taho ne a kan babura 200, kowanne mutum uku a kai, suka afka wa kauyen.

Ya ce:

“An kai gawarwakin sojojin 13, yan sanda biyar da dan vigilante daya da suka mutu a fadan zuwa Zuru a safiyar yau.”

“Muna kyautata zaton yan bindigan da suka kashe yan vigilante ne suka kawo mana harin.”

Yan bindiga da miyagu sun dade suna adabar garuruwa a yankin arewa maso yamma da tsakiya na tsawon shekaru, suna kisa, sata da garkuwa da kone-kone.

Saurari karin bayani …

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here