‘Yan Bindiga Sun Tarwatsa Taron Mambobin Jam’iyyar LP a Enugu

 

Tsagerun yan bindiga sun sake tarwatsa taron mambobin jam’iyyar LP wacce Peter Obi ke takarar shugaban kasa a Enugu.

Rahotannin da aka tattara sun nuna cewa maharan sun buɗe wuta a iska bayan kutsa wa wurin a Umuida, ƙaramar hukumar Igbo-Eze ta arewa.

Wata majiya tace maharan sun kona mota, Babura da kuma Keke-Napep da suka taras a wurin.

Enugu – A ranar Lahadi da ta gabata, wasu ‘yan bindiga suka tarwatsa taron jam’iyyar Labour Party (LP) ta Peter Obi a Umuida, ƙaramar hukumar Igbo-Eze ta arewa jihar Enugu.

Vanguard ta ruwaito cewa yan bindigan sun isa wurin a Babura biyu, suka buɗe wuta a saman iska, suka tarwatsa mambobin jam’iyyar kana suka babbake motoci, Napep da Baburan wurin.

Wata majiya da ta nemi a sakaya bayananta, tace harin ya auku ne a wuraren taruka biyu, Umu Aji da Nkwo Iyida inda magoya bayan LP ke ganawa da juna.

Majiyar ta kuma nuna damuwarta bisa yawaitar kai wa mambobin jam’iyyar LP hari yayin da suke gudanar da taro, inda ta ƙara da cewa mai yuwuwa lamarin na da alaƙa da siyasa.

Majiyar ta ce:

“Muna tsaka da taro lokacin da wasu mutum huɗu a kan Babura biyu suka iso wurin, suka fara harbe-harben bindiga a saman iska, nan take kowa ya yi takansa domin tsira.”

“Shugaban gunduma da wasu mambobi suka gudu suka bar Makullan motocinsu a kan Teburi, mun gano maharan sun ƙona Babura da Keke-Napep. Sannan kuam sun tafi da wata Mota Camry.”

“Bayan wani ɗan lokaci, sakamakon wata matsala injin Motar ya tsaya, mutum biyu daga cikin maharan suka fito daga cikin motar suka ƙona ta gabanin su kama gabansu.”

Duk wani yunkurin jin ta bakin kakakin hukumar yan sandan Enugu, Daniel Ndukwe, bai kai ga nasara ba domin ba ya ɗaga kiran waya ko amsa sakonnin da aka tura masa kan lamarin.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here