IPOB: Rundunar ‘Yan Sanda ta Kama Mambobin ƙungiyar 16 da Bindigu da Bama-Bamai

 

Wasu da ake zargin mambobin IPOB ne dake da hannu wajen ta’addanci a yankin kudu maso gabashin Najeriya sun faɗa komai hukunar yan sanda.

Rundunar ‘Yan sanda ta bayyana cewa waɗan da aka kama ɗin nada hannu a kisan da ake yima jami’an tsaro da kuma wasu ta’addanci a yankin

Yan sandan sun kuma ce suɓ kwato makamai masu hatsari daga mambobin IPOB ɗin da suka cafke.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke mambobin ƙunguyar dake ikirarin kafa ƙasar biyafara IPOB 16 da kuma kwato bindigu da bama-bamai a hannunsu.

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da mai magana da yawun rundunar, Frank Mba, ya fitar a ranar Lahadi 28 ga watan Maris, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Hukumar yan sandan ta zargi waɗan da aka kama ɗin da haɗa baki wajen tada rikice-rikice da kuma kai hari ga jami’an tsaro da kayayyakinsu a yankin kudu maso gabashin Najeriya da ma wasu sassan ƙasar nan.

Legit.ng ta gano cewa an sami wannan nasarar ne bayan aikin haɗin guiwa tsakanin yan sanda, sojojin ƙasa, da sojojin sama domin kamo mutanen da ke da alhakin kai ma jami’an tsaro hari da kuma bata wurare da kayayyakin jami’an.

Waɗan da aka kama sun haɗa da; Ugochukwu Samuel, ɗan shekara 28 daga karamar hukumar Arochukwu Jahar Abia; Raphael Idang, ɗan shekara 31 ɗan karamar hukumar Odukpani jahar Cross River.

Sauran sun haɗa da Cletus Nwachukwu Egole, ɗan kimanin shekara 60, ɗan garin Orlu jahar Imo; da kuma Michael Uba, shima ɗan jahar ta Imo.

Sai dai ba’a bayyana sauran mutum 12 ba.

‘Yan sandan sun bayyana cewa, binciken da suka gunar ya nuna mutanen na da hannu a mafi yawancin tashin hankullan da aka yi a yankin kudu maso gabashin ƙasar nan.

“An kama waɗan da ake zargin a sassa daban-daban na ƙasar nan bayan juriya, da kuma saka fasaha a aikin.” A cewar mai magana da yawun yan sandan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here