Manyan ‘Yan Sandan da Akai Garkuwa Dasu Sun Samu ‘Yanci

A cikin makon nan ne aka samu labarin cewa ‘yan bindiga sun sace wasu manyan jami’an ‘yan sanda a tsakanin Katsina zuwa Asabar.

An samu labarin sace manyan jami’an ne ta hannun matar daya daga cikinsu bayan ya kira, ya bukaci a siyar da gidansa a biya kudin fansa.

Sai dai, a cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sanda ta fitar ranar Juma’a, Frank Mba, ya ce an kubutar da dukkan jami’an.

Rundunar ‘yan sanda ta sanar da cewa an kubutar da manyan ‘yan sanda tara, dukkansu ASP, da aka sace tun ranar takwas ga watan Nuwamba na wannan shekarar a tsakanin jihar Katsina da Zamfara.

An sace manyan ‘yan sandan ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, Maidugurin jihar Borno.

A cikin wani jawabi da kakakin rundunar ‘yan sanda, Frank Mba, ya fitar ranar Juma’a, ya ce wani binciken karkashin kasa da suka gudanar, bayan samun labarin sace jami’an, ya gano wurin da aka garkamesu.

An sace jami’an a tsakanain garin Kankara zuwa Sheme a jihar Katsina sakamakon mummunan harin da wasu ‘yan bindiga sanye da kayan soja suka kai a kan motar haya da suke ciki tare da wasu fararen hula.

“Rundunar ‘yan sanda ta samu nasarar kubutar da manyan jami’anta guda tara da aka sace tun ranar 8 ga watan Nuwamba a tsakanin garin Kankara da Sheme a jihar Katsina yayin da suke tafiya a cikin motar haya da tsakar dare.

“Basa dauke da makamai, kuma basa sanye da kakin aikin dan sanda.

“Wasu ‘yan ta’adda, dauke da manyan bindigu, da ake zargin ‘yan bindiga ne, kuma sanye cikin kakin sojoji, su ne suka sacesu bayan sun kai wa motarsu farmaki yayin da suke tafiya cikin tsakar dare.

“Dukkaninsu masu mukamin ASP ne kuma suna kan hayarsu ta zuwa Gusau, jihar Zamfara, daga Maiduguri, jihar Borno a lokacin da tsautsayin ya faru,” a cewarsa.

Mba ya ce biyu daga cikin jami’an yanzu haka suna asibiti ana duba lafiyarsu, yayin da sauran bakwai suna samun kulawa ta musamman.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here