Sakamako CGPA 7.0: ‘Yar Najeriya ta Samu Tallafin Karatu Zuwa Amurka

Wata kwararriyar yar Najeriya, Ofure Ebhomielen, ta baiwa mutane mamaki a lokacin karatun ta na digirin farko a jami’ar Ibadan (UI).

Matar ta bayyana cewa babu wani ƙarshen zangon karatun jami’a da baza ta ci sakamako CGPA 7.0 ba, ta ce har a aji na uku wanda yafi bata wahala.

Amma yanzun zata zama ɗalibar Standford, ɗalibar ta ce karatu a ƙasashen waje yafi sauƙi sosai babu takura akan na Najeriya.

Wata matashiya yar Najeriya, Ofure Ebhomielen, ta karya tarihin fita da sakamako a jami’ar Ibadan (UI) a matsayin ɗaliba mace ta farko da ta ci 7.0 a gaba ɗaya sakamakonta har ta gama jami’ar.

A wata zantawa da tayi da Legit TV, Ofure ta bayyana cewa ita ce ɗaliba ta huɗu data sami makamancin wannan sakamakon.

Bayan wannan babbar nasarar da ta samu Ofure ta sami tallafin cigaba da karatunta na digiri na biyu a jami’ar Standford, Amurka.

A lokacin karatunta a UI, Ofure ta ce yan uwanta ɗalibai sun santa ne sanda tazo aji na biyu, daga nan ta fara taimaka ma ɗalibai wajen karatunsu.

Ɗalibar mai basira ta iya tuna lokacin data fusakanci babban ƙalubale a ajinta na uku a darasin lissafi (Mathematics).

Ta ce, wani abokin ta, Olawale Ahmed, shine ya koya mata darasin.

Da aka tambayeta ko ya taji da ta sami tallafin karatu zuwa Amurka, Ofure ta bada amsa cikin barkwanci inda ta ce:

“Na cike neman takardar izinin karatun (Admission), amma sai da na faɗa ma mai kula damu a jami’a cewa bazan iya ɗaukar nauyin wannan karatun ba sabida canjin dala zuwa naira ya tashi sosai.”

Ofure ta ce tallafin karatun ya iso gareta ne a lokacin da take cin abinci.

Ta ƙara da cewa karatu a Amurka yana da wahala sabida a cewarta zata ji kamar an tsuke ta ne idan ta ɗauki darasi biyu kacal a zangon karatu.

Ba kamar a Najeriya ba ind take iya ɗaukar darussa 14 a zangon karatu ɗaya.

Daga ƙarshe, Ofure ta bayyana matakan samun nasara da suka haɗa da aikin gida, gwaji akai-akai sune hanyoyin da ɗalibai ke sanin inda suka dosa a sakamakon su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here