Ku Zabi Wadanda Suka yi Yunkurin Magance Matsalolinku – El-Rufai

 

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya shawarci yan Najeriya kan shugabannin da ya kamata su zaba gabannin zaben 2023.

El-Rufai ya bukaci al’ummar kasar da su zabi wadanda suka yi kokarin magance matsalolinsu koda kuwa basu magance su ba don sun fi wadanda suka haddasa su.

Ya jinjinawa hukumomin tsaro a kan yadda suka kaddamar da hare-hare kan yan ta’adda da makiyan jihar Kaduna.

Kaduna – Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa munanan hare-haren da sojoji ke ci gaba da kaiwa kan yan ta’adda da makiyan jihar zai kare Kaduna.

El-Rufai wanda ya yi jawabi a taron kaddamar da littafin Kaduna na 4, ya jinjinawa kokarin hukumomin tsaro wajen maganin masu aikata laifuka a jihar.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan na Kaduna ya bukaci al’ummar kasa da su zabi shugabannin da za su magance matsalolinsu.

El-Rufai ya ce:

“Ku zabi wadanda suka yi yunkurin magance matsalolinku koda basu magance su ba sunfi wadanda suka haifar da su.

“Mun yi nadama cewa saboda lamarin jirgin kasa, har yanzu babu jirgin kasan Abuja-Kaduna, amma a cikin makonni shida da suka gabata, an samu ci gaba a farmakin da ake kaiwa wadannan miyagun kuma muna da karfin gwiwa idan aka ci gaba, a lokacin da za ku dawo taron KABAFEST 5, za ku tuko motarku zuwa Kaduna ba tare da kowani tsaro ba ko daukar jirgin kasa.”

Gwamnan ya yi godiya ga wadanda suka shirya taron, yana mai cewa KABAFEST na da muhimmanci din nuna farin Kaduna sabanin abun da mutane ke fadi game da jihar.

Ya kara da cewa:

“Abin da ya kamata shi ne sanya kowa a zuciya, ta yadda duk wanda ya so zai zauna, ya yi aiki da kuma biyan haraji a matsayin dan Kaduna saboda makomar Kaduna tana hannun matasa, musamman mata, kuma mun kuduri aniyar ba su damar samun ci gaba.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here