Zamfara: An Ceto Wasu ‘Yan Matan Katsina Daga Hannun ‘Yan Bindiga
Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da kubutar da wasu ‘yammata 26 da ‘yan bindiga suka sace tare da yin garkuwa da su.
Ceto ‘yammmatan na daga cikin nasarorin da jihar Zamfara ta samu a cigaba da yin sulhun da ‘yan bindiga.
Wannan ceto ƴanmatan da aka yi yasa adadin mutanen da ƴan bindiga daɗin suka saka ya kai sama da arba’in 40 daga wancan satin Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya ce kwalliya tana biyan kuɗin sabulu a tattaunawar sulhun da ake yi da ƴanbindiga daɗi a jihar, sakamakon sakin ƴanmata 26 ƴan asalin jihar Katsina wanda dukkan su yara matane masu ƙarancin shekaru.
An saki ƴanmatan ga gwamnatin jihar Zamfara ba tare da biyan kuɗin fansa ba, a cewar mai magana da yawun gwamna, Zailani Baffa.
Read Also:
An sace ƴanmatan daga ƙaramar hukumar Faskari jihar Katsina, kuma an kawo su jeji cikin jihar Zamfara.
Sai cikin sa’a gwamnatin Zamfara ta samu nasarar ganosu tare da ceto su ta hanyar haɗinguiwa da ƴan bindigar, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Abubakar Dauran.
Kwamishinan ne ya wakilci gwamna Matawalle a tattaunawar sulhu da ƴan bindigar a ƙoƙarin tabbatar da tsaro da kuma zaman lafiya a jihar.
Gwamna Matawalle, wanda ya karɓi kuɓutattun ƴan matan, ya ce gwamnatinsa ba zata yi watsi da tattaunawa don wanzar da zaman lafiya ba.
“Waɗanda suka yarda cewa bamu yi dai-dai ba da muka yi sulhu da ƴan bindigar, basu san cewa kuɓutar da ƴanmatan, ba karamar nasara ce marar misaltuwa ba”.
Ceto ƴanmatan ya kara adadin ƴammata da mutanen da aka ceto zuwa sama da arba’in daga makon da ya gabata.