Biki a Keken Guragu: Amarya ta Karye Ana Sauran Sati ɗaya Bikin ta

 

Wata budurwa ƴar Najeriya wacce akai aurenta tana kan keken guragu ta sha yabo sosai a yanar gizo.

Budurwar wacce ke da aukin jiki ta faɗi wanda a sanadiyyar hakan ƙafarta ta karya ana sauran sati ɗaya bikin ta.

Duk da wannan koma baya da ta samu, budurwar ta samu ta halarci bikin nata cikin wata shiga wacce ta ƙayatar.

Wata budurwa ƴar Najeriya ta ƙare da yin aure akan keken guragu bayan ta faɗi ta samu karaya a ƙafarta.

Wata ta kusa da amaryar sabon aure wacce ta sanya bidiyon bikinta a TikTok, ta bayyana cewa budurwar faɗi ne ana sauran kwana bakwai bikin ta.

Ta bayyana cewa shaiɗan ya makaro inda ta miƙa godiyar ta ga ubangiji bisa yadda akai bikin cikin nasara duk kuwa da koma bayan da amaryar ta samu.

Ta sanya bidiyon yadda aka gudanar da bikin a cikin coci inda take cewa, nufin ubangiji ne yiwuwar auren.

Mutane da dama a yanar gizo sun yabawa jarumtar amaryar da mijinta inda suka nuna godiyar su ga ubangiji bisa nasarar da ya bayar tayin auren masoyan biyu.

Ga kaɗan daga ciki:

EVERYTHING LOLU ta rubuta:

“Wannan cikakken namiji ne, kai akwai daɗi namiji ya so ka fiye da yadda kake son shi oo.”

dallahs ta rubuta:

“Ƴar’uwata, tabbas shaiɗan ya makara. Zai cigaba da makara a koda yaushe.”

jummy ta rubuta:

“Wannan cikakken namiji ne ooo. Ina taya ku murna, na ji muku daɗi sosai, ubangiji ya albarkaci auren ku.”

Olahipsy ya rubuta:

“Karaya a ƙafa tana da matuƙar wahala”

tiwa la porch ta rubuta:

“Ina taya ku murna, na ji muku daɗi sosai, nima ina addu’ar ubangiji ya bani muradin zuciya ta.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here