Marigayi Attahiru ya Kama Hanyar Sanya ƙasar mu Alfahari Bisa Namijin ƙoƙarin da Yake yi Wajen Magance Matsalar Tsaro – Buratai
Tsohon shugaban rundunar sojoji, Tukur Buratai, yayi alhinin rasuwar Janar Ibrahim Attahiru a hatsarin jirgin sama.
Buratai yace magajin nasa ya ɗakko hanyar da zai sanya Najeriya alfahari a ɓangaren tsaron da take fama da shi.
A ranar Jumu’a, shugaban rundunar sojojin ƙasa, Janar Ibrahim Attahiru ya rasa rayuwarsa a wani hatsarin jirgin sama da ya ritsa dashi a Kaduna.
Tsohon shugaban rundunar sojoji, Tukur Buratai, yace magajin sa, Ibrahim Attahiru, ya kama hanyar sanya Najeriya alfahari.
Mr. Buratai yace marigayin ya ɗakko hanyar kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a ƙasar nan kafin wannan mummunan lamarin yayi sanadiyyar mutuwarsa, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Read Also:
Ya bayyana hatsarin da abin tausayi ga yan Najeriya, yace Mr. Attahiru da jami’an da suka rasu tare da shi sun bar tarihin da ba za’a taɓa mantawa dashi ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
A cewarsa, hatsarin yayi matuƙar girgiza shi kamar yadda ya girgiza yan Najeriya saboda Mr. Attahiru ya mutu amma yabar mutane da yaƙinin irin nasarorin da ya samu a ɓangaren ayyukan sojoji.
Buratai yace:
“Attahiru ya kama hanyar sanya ƙasar mu alfahari bisa najimin ƙoƙarin da yake yi wajen magance matsalar tsaron da muke fama da ita, bani da tantama a kan ƙwazon shi saboda yayi aiki a ƙarƙashina a ɓangare daban-daban.”
“Nayi matuƙar kaɗuwa da baƙin cikin mutuwar Janar Ibrahim Attahiru, a hatsarin jirgin sama, wanda ya riƙe muƙamai da dama kafin zaman shi shugaban rundunar sojoji.”
“A madadin iyalaina ina miƙa saƙon ta’aziyya ga shugaban ƙasa Buhari, iyalan shi, ministan tsaro, jami’an sojin ƙasa da na sama bisa mutuwar waɗannan manyan jami’ai yayin da suke cikin aiki.”
Buratai ya roƙi hukumomin tsaro su tabbatar da ayyukan da waɗannan mutanen suka ɗakko bai tafi a banza ba, ta hanyar cika musu burinsu a ayyukan da suka fara.