Bata Gari Sun Kai Hari Rumfar Zabe, Sun Kona Akwatunan Zabe

 

Jihar Legas – Wasu yan daba dauke da bindigu sun kai hari rumfunan zabe a Oshodi da Itire a Legas, inda suka kona akwatunan zabe.

Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun taho ne sanya da bakaken tufafi da face mask misalin karfe 11.30 na safiyar ranar Asabar

Wasu masu zabe da ba su iya tserewa ba a lokacin da yan daban suka iso sun jikkata.

Wasu majiyoyi sun ce yan ta’addan sun kai farkamin ne yan mintuna bayan jami’an tsaro da ke aikin zabe sun bar wuraren. A cewar wani Tajudeen Haruna, bayan yan mintuna, yan daban sun bude wuta don tsorata masu zabe.

Ya cigaba da cewa:

“Daga baya ne yan ta’addan suka cinna wa akwatin zaben da sauran kayan zabe wuta.”

Hakazalika, wasu yan ta’adda sun kai hari a unguwar Itire, misalin karfe 12 na rana, suka tsorata mutane da masu zabe a yankin.

James Nwoke, ya yi ikirarin cewa an yi hakan da gangan ne don haka wasu mutane zabe

Amma, akwai yan sanda da dama da sojoji a birnin Legas a ranar Asabar don kiyayye rushewar doka da oda.

A bangare guda, wasu matasa sun mayar da hanyar Agege da Apapa-Oshodi da wasu yankunan Ago palace zuwa filin kwallo.

Ana zullumi a mafi yankuna da ke Ago, Isolo da Ire-Akri bayan wasu sun gaza gana akwatunan zaben su.

Dakaci karin bayani …

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here