‘Yan Daba Sun Tarwatsa Masu Zabe a Legas

 

Jama’a sun shiga tashin hankali a yankin Ikate da ke jihar Lagas bayan wasu bata gari sun far masu a wajen zabe.

Yan daban sun lalata tare da sace kayan zabe bayan sun fatattaki jama’a da jami’an hukumar zaben.

A yau Asabar, 25 ga watan Fabrairu ne ake gudanar da zaben shugaban kasa da na yanmajalisun tarayya a fadin Najeriya.

Lagos – Masu zabe a yankin Ikate da ke jihar Lagas basu samu damar aiwatar da yancinsu na yan kasa ba ta hanyar yin zabe a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

Hakan ya kasance ne bayan wasu bata gari da ake zaton yan dabar siyasa ne sun farmaki rumfar zabensu sannan suka fatattaki jama’ar da suka taru domin yin zabe tare da lalata kayan zaben.

A cewar wasu da abun ya faru a kan idanunsu, lamarin ya shafi rumfar zabe ne da ke kusa da fadar sarkin Elegushi, jaridar Vanguard ta rahoto.

Sai mun yi zabe za mu tafi, masu kada kuri’a

Sai dai kuma, masu kada kuri’ar da ke kokarin takewa yanci sun dage lallai sai sun aiwatar da yancinsu kafin su bar rumfar zaben.

PM News ta kuma rahoto cewa rumfunan zabe hudu yan daban suka farmaka kuma hakan ya haifar da tashin hankali a yankin inda mutane suka dunga gudun tsira.

An kuma tattaro cewa maharan sun tsere da akwatunan zabe sannan suka fatattaki jami’an hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here