ɓatagari Sun Tarwatsa Ma’aikatan Zaɓe da ‘Yan Jarida a kano
Rahotanni daga Kano a Najeriya sun bayyana cewa an samu wata hatsaniya a mazaɓar Ja’oji har wasu ma’aikatan zaɓe da ƴan jarida suka sha da ƙyar.
Wakilin BBC wanda ya kasance cikin ƴan jaridar da suka ɓuya a wani aji tare da malaman zaɓe, ya ruwaito cewa ɓatagarin sun kutsa cikin mazaɓar ne a dai-dai lokacin da jami’an INEC ke shirin fara ƙirgen ƙuri’u bayan da aka kammala zaɓe a mazaɓar.
Read Also:
Lamarin dai ya sa dole aka dakatar da aikin har zuwa lokacin da lamarin ya lafa.
Wakilin na BBC ya tabbatar da cewa mutanen da ke mazaɓar sun nemi mafaka a wata makaranta a lokacin da suka ga ɓatagarin.
Ya ce ya hango ƴan daban ɗauke da muggan makamai sun kai kawo a mazaɓar, inda ya ce sun tafi da na’urar VBAS guda ɗaya daga mazaɓar.
A cewarsa, jami’an tsaro ba su isa wajen ba a lokacin da ɓatagarin suka shiga mazaɓar.
Tuni dai aka samu lafawar al’amarin inda kuma aka soma ƙirgen ƙuri’un a wannan mazaɓa.