Za mu Buga Wasan ƙwallon ƙafa da Tubabbun ‘Yan Daba – CP Muhammed Gumel

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano (CP), Muhammed Usaini Gumel, ya ce hukumar za ta shirya wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar ta da wasu ‘yan daban da suka tuba, a wani mataki na tabbatar da gaskiyar tubansu.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wasu mutane 108 da aka kama da laifuka daban-daban a lokacin bikin Sallah da ya gabata.

Ya ce, “Za mu bullo da wata hanya ta daban don tabbatar da cewa wadannan ‘yan daban suna canza rayuwarsu tare da zama mutanen kirki. Har ma za mu shirya gasar wasanni da su. Za mu buga wasan ƙwallon ƙafa.

“Yanzu za mu mayar da hanalin mu da idanunmu kan ayyukan ‘yan daba (daba) da ke kunno kai, musamman a cikin babban birnin Kano”, in ji Kwamishinan.

CP Muhammed ya ƙara da cewa sun tsara dabarun aiki da kuma ingantaciyar hanyar tara bayanan sirri domin magance duk wani nau’in laifi da ake aikatawa a ciki da wajen jihar Kano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here