ƙwauron Maki: An ɗaure Matashin da ya Kashe Malamarsa

 

An yi wa wani matashi a jihar Amurka ta Iowa ɗaurin rai-da-rai bayan ya yi wa malamarsa dukan kawo wuƙa da sanda har ya zama ajalinta.

Willard Miller, ɗan shekara 17, ya amsa laifin aikata kisa a watan Afrilu saboda hannun da yake da shi wajen kashe Nohema Graber, wata malamar harshen Sifaniya ranar 2 ga watan Nuwamban 2021.

Miller da abokin da aka zarge su tare, Jeremy Goodale, wanda yanzu ya cika shekara 18, sun auka wa Nohema Graber mai shekara 66, bayan ta bai wa Miller maki kaɗan a makaranta.

Yana da shekara 16 lokacin da suka aikata kisan kan, amma an tuhume su a matsayin baligai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here