Shugaba Buhari na Daya Daga Cikin Musulmai 500 Mafi Karfin Masu Fada a ji a Duniya

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na cikin jerin musulmi masu karfin fada aji a duniya, kamar yadda cibiyar nazarin addinin Islama da ke Amman a Jordan ta bayyana.

Duk shekara cibiyar na wallafa sunayen musulmi 500 masu karfin fada aji a duniya.

Kuma a bincken da ta wallafa karo na 12 cibiyar ta ce Shugaban Najeriya Muhammadu ne na 16 a jerin musulmi ƙarfin fada a ji a a duniya.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ne musulmi mafi ƙarfin faɗa a aji a duniya. Sarki Salman na Saudiyya ne na biyu a duniya.

Jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei ne na uku a jerin musulmi masu karfin fada a ji a duniya.

Cibiyar ta ce yawan musulmi a duniya an kiyasta cewa ya kai biliyan 1.9, kashi 26 na yawan al’ummar duniya.

Babban Shehin Malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Ibrahim Saleh shi ne na 48 a duniya.

Sauran ƴan Najeriya da ke cikin jerin musulmi masu karfin fada a ji a duniya sun hada da Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero.

Akwai kuma Shehin malamin Tijjaniya Sheikh Dahiru Bauchi da jagoran ƙungiyar Shi’a ta IMN Malam Ibrahim Zakzaky da kuma attajirin Afrika Alhaji Aliko Dangote.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here