Shugaba Buhari ya Tafi da Kowane Bangare na Kasar nan a Mulkinsa – Uchenna Orji

 

Dave Umahi yana nan a kan bakarsa na rokon Ubangiji ya kawo wa wani irin Buhari.

Wannan magana da gwamnan Ebonyin ya yi, ya jawo masa raddi daga Nyesom Wike.

Kwamishinan labaran jahar Ebonyi ya kare gwamnan, ya yabawa gwamnatin Buhari.

Abakaliki – Kwamishinan harkokin yada labarai da wayar da kan al’umma na jahar Ebonyi, Orji Uchenna Orji, ya jaddada maganar da David Umahi yayi.

Barista Orji Uchenna Orji yace Mai girma gwamnan Ebonyi, David Umahi bai yi nadamar kalaman da ya yi a game da samun irin Muhammadu Buhari a 2023 ba.

Daily Trust tace Uchenna Orji ya shaida wa manema labarai cewa ganin yadda Buhari yake shawo kan matsalar tsaro, shiyasa yace a roki wani irinsa.

“Saboda haka ina tunanin ta ko ina, Gwamna Dave Umahi yayi daidai, saboda idan ka duba kiraye-kirayen da ake yi na addini da kabilanci, da a ce ba mutum mai dattaku irin Buhari ba ne, da abubuwan sun fi haka muni.”

“Kafin ya hau mulki, ‘yan bindiga sun cika babban birni, amma da ya shiga ofis, mun daina jin labarin ta’adin wadannan ‘yan bindiga a Birane, saboda haka ya yi kokari.”

Kwamishinan yada labaran yake cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo tsare-tsaren taimaka wa marasa galihu a karkashin babban banki na CBN.

Sannan a cewar Uchenna Orji, shugaban Najeriyar ya tafi da kowane bangare na kasar nan a mulkinsa.

Jaridar ta rahoto Kwamishinan yana bayani game da ziyarar da Buhari ya kai Imo, yace mutane sun zauna a gida ne saboda tsaro ba don yi wa IPOB ladabi ba.

“Sha’anin rashin tsaro ba matsalar gwamnatin nan mai-ci ba ce, gwamnatin baya da wasu masu ruwa-da-tsaki a gwamnatin nan suka kawo ta.”

“Ba na cikin gwamnati kadai ba, har da wadanda ba su cikin masu rike da madafan iko.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here