Sarkin Musulmai ya yi Kira ga Dukkan Kabilun Najeriya da su Hada Kansu

 

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira ga yan Nigeria su so juna su kuma hada kai.

Sultan din ya yi wannan kiran ne a wurin wani taro a Abuja yana mai cewa Allah bai yi kuskure ba da ya hada mu zama tare.

Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi zargin wasu na neman amfani da addini don raba kasar amma ya ce ba za suyi nasara ba.

Abuja – Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na III, ya bukaci dukkan kabilun Nigeria su cigaba da zama a matsayin yan uwan juna domin Allah bai yi kuskure ba da ya hada mu zama a matsayin kasa daya, Daily Trust ta rawaito.

Da ya ke jawabi a matsayinsa na shugaba a wurin taron bada lambar yabo na shugabanci na 2020 a ranr Alhamis a Abuja, Sultan ya ce raba kasar ba zai magance matsalolin da kowace kabilar ke fama da shi ba amma hada kai tare a warware matsalar ce ta fi amfani.

Sultan din ya ce:

“Idan muka rabu kowa ya kama gabansa, ta yaya za mu rayu?

Allah bai taba kuskure ba kuma baya kuskure, wannan shine kaddararsa kuma ya kamata mu rungume kadarar.

“Hada mu a matsayin yan Nigeria ba kuskure bane kuma wannan shine abin da Allah ya so. Idan yana son wani abin daban da tuni ya yi don haka ya kamata mu rungumi addinan mu a matsayin musulmi da kirista.

“Dukkanmu mun san daga mahallici daya muke.”

Sultan ya ce wadanda ke amfani da addini domin raba kan mutane ba za su yi nasara ba domin mutanen kasar ba za su biye musu ba.

Ya kuma shawarci yan Nigeria su bada gudumawarsu don ganin an samar da tsaro a kasar.

Abin da Osinbajo ya ce wurin taron?

A jawabinsa, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce bai amince da batun da wasu ke yi ba na cewa hada mu da turawan mulkin mallaka suka yi ya hana kasar cigaba kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

a ce tarihi ya nuna cewa yankunan suna huldar kasuwanci da juna don haka ba baki bane. Amma ya ce akwai laifin shugabanni da suka gaza gina hukumomi da za su kula da al’umma.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here