Ni Kwarraren Likita ne Kuma Soja Saboda Haka Nasan Abinda Nake Fada – Sheikh Gumi

 

Sheikh Ahmad Gumi yayi martani ga mai magana da yawun shugaban kasa.

Malamin yace shi kwarraren Likita ne kuma Soja saboda haka ya san abinda yake fada.

Gumi ya shahara da tofa albarkacin bakinsa kan lamarin tsaro a Najeriya.

Shahrarren Malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya sake kira ga gwamnatin tarayya cewa ta rungumi sulhu da yan bindiga saboda yaki ba zai kawo karshen matsalar tsaro ba.

Gumi yace al’ummar jahar Zamfara da ake artabu yanzu da yan bindiga kawai ke shan wahala saboda tuni yan bindigan sun gudu, kamar yadda ya daura a shafinsa na Facebook.

Ya ce yan bindigan yanzu sun fara shiga garuruwan da ko hanya basu sani ba amma duk da haka suna cigaba da aikata laifin garkuwa da mutane saboda haka korarsu daga Zamfara ba zai yi amfani ba.

Yace:

“La’lla baku samu labarin cewa yan bindiga tuni sun samar da hanyoyin tserewa ruwan bama-baman Sojoji. Sun fada mana cewa sai dai ku kashe matanmu da yaranmu da hare-harenku.”

“Jiya (Alhamis), wasu gungun mutane biyu da harin yan bindiga ya shafa sun fada min cewa an sace yan uwansu a Kaduna – Rigachikun da Keke. Wani Injiniya da ya samu tsira yace da ya saurari yan bindigan ya fahimci cewa baki ne saboda yaji suna tambayar mutan gari hanya.”

“Maganar gaskiya Zamfara ta musu zafi yanzu, amma zasu koma wasu wurare. Shin za’a yanke duka hanyoyin sadarwa a Na

jeriya ne?.” Yayinda yake kara kira ga hukuma tayi sulhu da yan bindiga, yace “Yaki bai taba zama mafita ba a ko ina.”

Malam Gumi yayi martani ga mai magana da yawun shugaban kasa kan kalamansa na cewa yana tausayawa yan bindiga.

Gumi yace shi Malami addini ne mai digri 3, shi Likita ne kuma tsohon Soja; saboda haka don soyayyar kasa da al’umma yake abubuwan da yakeyi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here