Jami’an DSS Sun Kama Matashiyar da ta yi Barazanar Kashe Kanta, Gawuna da Alƙalan Ƙotun Kano

 

Jami’an DSS sun cafke matashiyar nan da ta yi barazanar hallaka Shettima, Gawuna da Alƙalan Ƙotun Kano kuma ta kashe kanta.

Fiddausi Ahmadu, ‘yar kimanin shekara 23 a duniya ta yi wannan barazana ne a wani faifan bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya.

Ta ce duk inda ta ga Gawuna ko shugabar alƙalan da suka kwace nasarar NNPP zata iya tashin bam kowa ya mutu.

Jihar Kano – Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta damƙe matar da ake zargin ta yi barazanar kashe kanta kuma ta kashe duk mai hannu a nasarar da APC ta samu a Kotun zaɓen gwamnan Kano.

Matar mai suna Fiddausi Ahmadu, ta yi barazanar cewa zata yi ƙunar baƙin wake ta kashe duk wanda ya taimaka ɗan takarar APC, Nasiru Gawuna, ya samu nasara a Kotu, sannan ta kashe kanta.

Leadership ta tattaro cewa idan baku manta ba, Kotun sauraron ƙararrakin zabe ta ayyana Gawuna a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano bayan soke wasu ƙuri’u.

A rahoton da muka kawo muku, Kotun ta umarci INEC ta janye Satifiket ɗin da ta bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP, kana ta bai wa Gawuna sabon shaidar cin zaɓe.

Su wa matashiyar ta yi wa barazana?

A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, matashiyar yar shekara 23 a duniya ta yi iƙirarin cewa zata yi yaƙin kwato haƙƙin NNPP da Gwamna Abba Gida-Gida.

A faifan bidiyon, an ji Fiddausi a harshen Hausa tana barazana ga shugabar kotun, inda ta yi gargadin cewa duk inda ta ga Alkalin, ita (Fiddausi) ba za ta damu ba ta tashi bam su mutu baki ɗaya.

Har ila yau, Fiddausi ta gargadi Gawuna, tana mai cewa, “Kada ka kuskura na gano inda kake, zan ɗaura Bam da ni da kai mu mutu baki ɗaya ba.”

Ta kuma caccaki mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Ƙashim Shettima, inda ta kira shi da sunaye daban-daban tana zarginsa da kitsa manaƙisar raba NNPP da mulkin Kano.

A cewarta, idan da za a tara mata Ganduje, Gawuna, Rarara da Alkalan da suka yanke hukunci a wuri ɗaya, zata iya shiga da Bam ta tashe su baki ɗaya, Daily Post ta rahoto.

“Zamu gurfanar da Fiddausi a gabam Ƙuliya saboda bai kamata a kauda ido a ɗauki wannan barazana da wasa ba,” inji wata majiya daga hukumar DSS.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com