Hukumar EFCC ta Kama Rochas Okorocha

 

Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan Imo Rochas Okorocha, kuma ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

EFCC ta tafi da Rochas daga gidansa da ke unguwar Maitama a Abuja da yammacin Talata.

Jami’an EFCC da ƴan sanda sun yi dirar mikiya tare da mamaye gidan tsohon gwamnan, inda rahotanni suka ce an yi harbi a ƙoƙarin kama shi.

Hukumar EFCC ta ce matakin ya biyo bayan ƙin amsa gayyatar da tsohon gwamnan ya yi bayan tsallake belin da ya samu a farko.

A ranar 24 ga watan Junairun shekarar 2022 ne EFCC ta shigar da kara a gaban kotu tana tuhumar Okorocha da laifuka 17 da suka hada da karkatar da kudaden al’umma da kadarori da suka kai naira biliyan 2.9.

Hukumar ta ce yunƙurin gurfanar da Sanata Okorocha sau biyu ya ci tura sakamakon ƙin amsa gayyatar da aka yi ma shi.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here