Ayodele Fayose ya Karbi Bakuncin Kashim Shettima
Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya karbi bakuncin Kashim Shettima da mutanensa.
‘Dan takaran na mataimakin shugaban kasa a APC ya ziyarci jigon ‘yan adawar a gidansa da ke Abuja.
Ana tunanin Sanata Shettima ya fara yi wa jam’iyya mai mulki zawarcin tsohon Gwamnan na PDP ne.
Abuja – ‘Dan takaran kujerar mataimakin shugaban Najeriya a APC, Kashim Shettima ya kai ziyara ta musamman zuwa wajen Mista Ayodele Fayose.
Kamar yadda Kashim Shettima ya sanar a shafukansa na sada zumunta, shi da kan shi ya je har gidan tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose.
A yammacin Talata ne Sanata Shettima ya je gidan Fayose, kuma an ga sun dauki hotuna cikin fara’a, amma ba a san makasudin tattaunawar ba.
“Na kai wa ‘danuwa, tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Mai girma Ayodele Peter Fayose ziyara. Oshoko ya karbe hannu biyu-biyu cikin abokantaka.
“Na gode da goyon bayanka, Ubangiji ya yi maka sakayya da ka karbi bakunci na tare da ‘yan tawaga ta.
– Kashim Shettima
Read Also:
Me ya kai Kashim Shettima wajen Fayose?
Jaridar Premium Times ta ce wannan lamari ya jawo mutane su na tofa albarkacin bakinsu a kan shafin Facebook na tsohon Gwamnan na jihar Borno.
Kiran Fayose wanda ya yi suna wajen adawa ga gwamnatin APC da Muhammadu Buhari yake jagoranta da ‘danuwa ya sa ake tunanin ana zawarcinsa.
Fayose yana cikin gwamnonin da ke yakar Iyorchia Ayu a kan takarar Atiku/Okowa.
Rikicin cikin gidan PDP a Ekiti
Kwanan nan shugabannin PDP suka dakatar da wasu mabiyansa da ke takara, sannan aka ruguza majalisar shugabannin jam’iyya na reshen Ekiti.
Babu mamaki Shettima ya yi amfani da rikicin cikin gidan na PDP ne domin ya jawo Fayose zuwa jam’iyyar APC da nufin ya taimaka masu a zaben 2023.
Punch ta fitar da labarin ganawar, kuma har zuwa yanzu ba a ji komai daga bakin Fayose ba.
A tsige Festus Keyamo – PDP
Rahoto ya zo cewa Jam’iyyar PDP ta dage cewa sai an sauke Festus Keyamo SAN. A lokacin ne Shugaban kasa yake taya Ministan murnar cika shekaru 53.
Kwamitin yakin zaben Atiku Abubakar ya tuhumi Keyamo da cin amanar da aka damka masa.