‘Yan Majalisar Tarayya Sun yi Gargadin Cewa Ana Amfani da Sakamakon Gwajin Corona na Karya don damfarar ‘Yan Najeriya a Kasar Ghana
Majalisar wakilai ta nuna damuwa kan yadda wasu bata-gari ke samar da sakamakon rigakafin corona na karya.
Wannan lamari na faruwa ne a kasar Ghana yayin da kasar ke sanya ‘yan Najeriya biyan makudan kudade don killace.
Majalisar ta bayyana bukatar daukar matakin gaggawa don magance wannan matsala da ta kunno kai.
Abuja – Rahoton da Daily Trust ta fitar ya ce, ‘yan majalisar tarayya sun yi gargadin cewa ana amfani da sakamakon gwajin corona na karya don damfarar ‘yan Najeriya a kasar Ghana.
Sanata Ibrahim Oloriegbe (APC, Kwara) ya tayar da batun ne a cikin kudirin da sanata Sadiq Umar (APC, Kwara), Betty Apiafi (PDP, Ribas) da Chukwuka Utazi (PDP, Enugu) suka gabatar.
Yayin gabatar da kudirin, Oloriegbe ya lura cewa akwai alamar ayar tambata cewa ‘yan Najeriya da aka gwada aka ga lafiyarsu a cikin kasar sun kamu da Korona a Ghana
Ya ci gaba da cewa hukumomin Ghana galibi suna yiwa ‘yan Najeriya da ke ziyartar kasar killacewa na tsawon makonni biyu kuma ana sanya su biyan kusan N70,000 a kowace rana.
Read Also:
A cewar dan majalisar, ‘yan Najeriya da ke tafiya Ghana ko masu wucewa ta Ghana sun koka da yadda ake sanya su biyan kusan Naira miliyan daya yayin da suke kebe.
Ya ce idan ba a binciki zargin da kyau ba kuma ba a magance shi ba, za a ci gaba da barnar, ta haka ne za a kwace dukiyar ‘yan Najeriya ba bisa ka’ida ba a yayin da ake fuskatar kalubalen tattalin arziki a duniya.
Oloriegbe ya kuma lura cewa:
“Akwai matukar bukatar ci gaba da neman allurar rigakafi da sakamakon gwaji saboda manyan ‘yanci da za su baiwa mutane.
“Hakanan, ko yaushe ana iya samun mutanen da ba sa son jira allurar rigakafin su a hukumance, ko kuma sakamakon gwaji a hukumance – kuma mutane da ke cikin bukata na iya fadawa cikin wannan lamarin.2
Ya nuna damuwar sa cewa: “Idan ba a magance zargin mutane na samun da yin amfani da katunan rigakafin corona na karya don yin balaguro ba, yana iya haifar da mummunan sakamako ga ‘yan Najeriya masu katunan rigakafin corona na gaske daga balaguro zuwa kasar waje.”
Don haka, Majalisar Dattawa ta umarci kwamitocin ta kan Lafiya da su gudanar cikakken bincike kan zarge-zargen biyu na sakamakon gwajin Korona na karya da ake amfani da su don damfarar ‘yan Najeriya a Ghana da tsarin samun katunan rigakafin Korona na karya.