Shugaba Buhari ya Goyi Bayan Cire Gwamna Mai Mala Buni a Matsayin Shugaban Riko na APC- Gwamna El-Rufa’i

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya goyi bayan cire gwamnan Yobe Mai Mala Buni a matsayin shugaban riko na APC kamar yadda gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa’i ya bayyana.

A hirar da kafar talabijin ta Channels ta yi da shi ranar Talata, El Rufa’i ya ce gwamnan Neja Sani Bello ya samu goyon bayan Buhari da kuma gwamnonin APC 19.

Sannan ya ce Buhari ne ya ce a cire gwamnan Yobe Mai Mala Buni.

“Buhari ne ya bayar da umarnin a cire shi kuma aka aiwatar, yanzu gwamna Bello ne ya gaje shi,” kamar yadda El Rufai ya bayyana.

Ya ce Mai Mala Buni wanda ba ya ƙasar zai dawo ne a matsayin gwamnan Yobe amma ba matsayin shugaban jam’iyyar APC ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here