Gwamnan Jahar Ebonyi David Umahi ya ɗaukaka Kara Kan Tsige Shi Daga Mulki

Gwamnan jahar Ebonyi David Umahi da ke kudu maso gabashin Najeriya ya daukaka kara game da hukuncin wata babbar kotun tarayya wadda ta bayar da umurnin sauke shi daga mulki bisa sauya sheka da ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Takardar da suka gabatar ta daukaka karar, ta ce kotun ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke, saboda haka ne ya ce yana da ja da daukacin shari’ar.

Takardar ta ce kotun ta gaza bisa dogaron da ta yi da sashen na 68, da na 109 na kundin tsarin Mulki wanda dole gwamnan ya bar mukaminsa kasancewar ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP wadda aka zabe shi a karkashinta, zuwa jam’iyyar APC mai mulkin kasar, wanda hakan a cewar takardar tamkar watsi ne da wani hukunci da kotun kolin kasar ta taba yankewa, tsakanin ministan shari’a na Najeriya da tsohon mataimakain shugaban kasa Atiku Abubakar, inda ta ce babu wani tanadin kundin tsarin mulki da ya haramta wa shugaban kasa, ko mataimakinsa, ko kuma gwamnan, ko mataimakinsa daga sauya sheka daga wata jam’iyya zuwa wata.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here