Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya ta Maka ASUU a Kotu

Rikicin da ya barke tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ta rufe jami’o’i da yawa sama da watanni bakwai zai koma kotun masana’antu a ranar Litinin mai zuwa.

Kungiyar ASUU ta shiga yajin aikin ne tun ranar 15 ga watan Fabrairu domin nuna rashin amincewa da lalacewar ababen more rayuwa a cibiyoyi daban-daban, da kuma rashin kula da jin dadin mambobinta.

Wata majiya mai tushe a ma’aikatar kwadago ta tarayya ta shaida wa jaridar THISDAY da daddare cewa sashin da ke kula da harkokin kasuwanci na ma’aikatar ya shigar da kara a gaban kotun sasantawa da masana’antu da ke Abuja kuma za a fara sauraron karar ranar Litinin mai zuwa.

A cewar majiyar, “Gwamnatin tarayya ta shigar da kara a kotun masana’antu tana kalubalantar ci gaba da yajin aikin da malaman jami’o’in ke yi. Wannan ya yi daidai da sashe na 17 na dokar takaddamar ciniki.”

An dai yi ta tattaunawa a tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyar ASUU amma duk ya kare ba tare da cimma wani sakamako na gaske ba.

Sai dai daga karshe tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta yi tsami a ranar Talatar da ta gabata bayan da bangarorin biyu suka gana a ofishin hukumar jami’ar ta kasa da ke Abuja.
Gwamnatin tarayya ta ce ba za ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da ba za ta iya aiwatarwa ba.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya bayyana haka a lokacin wani taro na shugabannin jami’o’in tarayya da kuma mataimakan shugabannin jami’o’in tarayya, wanda aka gudanar a ofishin NUC.

Adamu ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi tawagar gwamnati da ke tattaunawa da ASUU kan sanya hannu kan yarjejeniyar da gwamnati ba za ta iya cikawa ba.

Ministan ya ce gwamnati ta yi wa kungiyar karin albashi na kashi 23.5 cikin 100 “ga dukkan nau’o’in ma’aikata a jami’o’in tarayya, in banda farfesa da za a yi bitar kashi 35 cikin 100. Ya ce gwamnati ta kuma yi alkawarin cewa za a samar da Naira biliyan 150 “a cikin kasafin kudin shekarar 2023 a matsayin kudaden farfado da jami’o’in tarayya, da za a ba wa cibiyoyi a cikin kwata na farko na shekara.”

Har ila yau, gwamnatin ta ce za a samar da Naira biliyan 50 “a cikin kasafin kudin 2023 don biyan basukan alawus na ilimi, wanda za a biya a farkon kwata na shekara.”

Sai dai ASUU da wasu kungiyoyin jami’o’i uku sun yi watsi da tayin, suna masu bayyana hakan a matsayin “rashin wadatar da bukatunsu da ake bukata don tunkarar kalubalen da ke fuskantar tsarin jami’o’in.” (YAU)

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here