Masu Ruwa da Tsaki Sun Nemi Gwamnonin da ke da Arzikin Fetur Suyi Bayanin Inda Suka Kai Kason Kudinsu

 

Gwamna Nyesom Wike ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta biya jihohin Neja-Delta wasu kudinsu.

Akwai kason 13% da ake warewa Jihohin masu arzikin fetur, wanda Gwamnoni suke bin gwamnatin tarayya.

Bayan Wike yace an biya wannan kudi, an fara tambayar abokan aikinsa abin da suka yi da kason jihohinsu.

Rivers – Tambayar da jama’a suke yi a halin yanzu shi ne ina jihohin Neja Delta suka kai bashin rarar arzikin man fetur da gwamnatin tarayya ta biya su.

The Nation ta kawo rahoto cewa biyo bayan jawabin da ya fito daga bakin Gwamna Nyesom Wike a makon jiya, mutane sun taso gwamnonin Kudu a gaba.

Mai girma Gwamna Nyesom Wike ya shaidawa Duniya Gwamnatin Muhammadu Buhari ta dawowa Ribas kudin da take bi bashi na kason fetur din ta.

Gwamnan na Ribas yace da wadannan makudan kudi ne ya gudanar da ayyukan a zo-a gani. Daga ciki har da katuwar makarantar horas a Lauyoyi da ya gina.

Ganin yadda Ribas ta ci moriyar kudin nan, masu ruwa da tsaki sun nemi sauran Gwamnonin da ke da arzikin fetur suyi bayanin inda suka kai na su kaso.

Amsar Gwamnatin Delta

Da aka tuntubi, Gwamnatin Ribas, Ifeanyi Okowa yace N30bn kadai suka iya karba daga N270bn da suke bin bashi a asusun kasonsu na rarar arzikin fetur.

Gwamnan ya yi bayani ta bakin babban sakataren yada labarasa, Olisa Ifeajika, yace tuni sun yi wa talakawa bayani suna bin N270bn daga 2010 zuwa yau.

A saurare mu – Bayelsa

Mutanen jihar Bayelsa sun nemi gwamnansu ya yi masu bayanin abin da yake jawo koma-baya a jihar duk da irin kudin da suke samu daga danyen fetur.

Da aka nemi Kwamishinan yada labarai na jihar Bayelsa, Ayibaina Duba, domin ya yi karin-haske a kan lamarin, jaridar tace bai iya daukar duk kiran waya ba.

Maxwell Ibiba wanda shi ne kwamishinan yada labarai ya yi alkawarin zai yi bayanin gaskiyar lamarin a yau. Har zuwa yanzu, ana sauraron bayaninsa.

A binciki Akwa Ibom – PAP

Babban jami’in tsarin PAP na kasa, Imoh Okoko ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta binciki inda aka kai kudin da ta biya jihohin, musamman a Akwa Ibom.

Okoko yace duk da dukiyar jihohin yankin suke da shi, babu cigaban kirki da za a iya nunawa a yankunan Eket, Ibeno, Eastern Obolo, Mbo, Ikot Abasi da Esit Eket.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here