NARD: Ba Zamu Janye Yajin Aiki ba Har Sai Mun Samu Tabbaci Mai Karfi Daga Osinbajo – Likitoci

 

Kungiyar likitoci mazauna kasa sun bayyana cewa, sun yi imanin Osinbajo zai magance damuwarsu.

Sun bayyana haka ne bayan ganawa da suka yi da mataimakin shugaban kasan jim kadan bayan nada shi wani mukami.

Sun bayyana cewa, ba za su dage yajin aikin da suke ciki ba har sai sun samu tabbaci mai karfi daga Osinbajo.

Abuja- Kungiyar likitoci mazauna kasa (NARD) ta amince da nadin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin shugaban kwamitin sake fasalin kiwon lafiya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar, a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba inda ta bayyana cewa shi kadai ne fatansu.

Dokta Okhuaihesuyi Uyilawa, shugaban NARD, ya fadi haka ne yayin da yake magana ashirin Channels TV na al’amuran yau da kullum, Sunrise Daily.

Uyilawa ya ce:

“Mataimakin shugaban kasa shine kawai fatan mu, mun hadu da shi a ranar Juma’a, kuma abin takaici, a ranar Asabar, muka samu alamar da ba daidai ba daga ministan kwadago, wannan na sirri ne. Ya yi kama da son kai a yanzu.”

Wadannan batutuwa na zuwa ne bayan da kungiyar ta gana da mataimakin shugaban kasa Osinbajo ta manhajar Zoom, inda kungiyar ta ce Osinbajo ne ya nemi su yi ganawar.

Da aka tambaye shi ko kungiyarsa ta yi imanin mataimakin shugaban kasa na da mutunci a idon kungiyar, shugaban NARD ya ce:

“Yana da mutunci, amana, kuma shi ne wanda na yi imani zai iya sa abubuwa su yi aiki.”

A nasa bangaren, mataimakin shugaban NARD, Adejo Arome, wanda ke tabbatar da ganawar Osinbajo da hukumar, ya shaidawa manema labarai ciki har da Legit.ng cewa sun gana ne ta hanyar amfani da manhajar Zoom a ranar Juma’a, 3 ga watan Satumba.

Arome ya ce mataimakin shugaban kasar ya nemi bayanai na farko kan abubuwan da ke faruwa.

A cewar Arome:

“Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya tuntube mu. Ya gana da shugaban jiya (Juma’a). Hakika ganawar ta Zoom ya yi da shugabanmu duk da cewa wasu daga cikin mu na can. Shi (Osinbajo) ne ya bukaci ganawar domin yana son samun bayanin abin da ke faruwa.

“Ya ce yana bukatar cikakkun bayanai na duk abin da ya faru. Ya yi tambaya cikin natsuwa kuma mun yi imani zai yi wani abu kuma mun yi imani cewa nan ba da jimawa ba, zai kira mu a hukumance.

“Mun ba shi bayanin. Bayanan da muka ba shi na farko ne kuma ingantattu. Muna da tabbacin cewa sauran jami’an gwamnati ba za su ba shi dukkan cikakkun bayanai game da batun baki daya ba.

“Ya gaya mana cewa baya son a warware batun yanzu kuma daga baya a sake wani yajin aiki.

“Ya ce yana son ya kawo karshen matsalar lokaci daya. Muna jiran ya gayyace mu a hukumance kuma mun tabbata cewa zai yi. Mun amince da hukuncinsa.”

Ba zamu dakatar da yajin aiki ba sai mun ji ta bakin Osinbajo

A bangare guda, Kungiyar ta sha alwashin cewa ba za ta dakatar da yajin aikin sama da wata daya ba ba tare da sa hannun mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo ba.

Osakhuesuyi Uyilawa, ya ce kungiyar za ta kira komawa bakin aiki ne kawai idan ta samu tabbaci daga Farfesa Osibanjo, Daily Sun ta rawaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here