Gwamnatin Jahar Imo na Shirin Tarbar Shugaba Buhari a Ranar Alhamis, 9 ga Watan nan

 

Yanzu haka an shirya komai don ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa jahar Imo a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba.

Yayin ziyarar tasa, shugaban kasar zai kaddamar da manyan ayyuka da gwamnatin Hope Uzodimma jagoranta tayi.

Jami’an gwamnatin jahar sun ce a shirye suke su tarbi shugaban kasar, yayin da ake ci gaba da kokarin ganin ziyarar ta zama ta tarihi.

Owerri – Kwamishinan yada labarai na Imo, Declan Emelumba, ya ce gwamnatin jahar na shirin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba a Owerri.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ba da rahoton cewa an shirya shugaban kasar zai kai ziyarar aiki zuwa Imo don kaddamar da wasu ayyukan da jahar ta aiwatar.

Emelumba ya ce shugaban zai kaddamar da muhimman ayyukan da Gwamna Hope Uzodimma ya fara a cikin watanni 18 da suka gabata.

Kalamansa:

“Mun shirya sosai don karbar bakuncin Shugaban kasa a Imo. An kammala duk wasu shirye-shirye.

“Da isowarsa, ana sa ran zai fara kaddamar da ayyuka, ciki har da hanyar Naze-Nekede-Ihiagwa-Obinze da titin karkashin kasa akan hanyar D-Tiger Owerri.”

Ya ce Buhari zai kuma kaddamar da titin Egbeada da sabbin dakunan majalisar zartarwa na jahar a gidan gwamnati, da sauran su.

Ya kara da cewa:

“Ziyarar tasa za ta baiwa ‘yan Imo damar gani da maraba da shugaban kasar.”

Tuni, babban birnin jahar, Owerri, ya riga ya dauki sabon salo, musamman kan manyan hanyoyin da ke sada mutum da wuraren ayyukan da za a kaddamar.

Ana sake gina titin da ke gaban Gidan Gwamnati, ana gyara manyan hanyoyi da kuma share su.

Jaridar Guardian ta rahoto cewa gwamnatin jahar Imo ta rufe bankunan da dama a jahar saboda bin umurnin da kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) ta bayar na zaman gida a ranar Litinin a duk yankin kudu maso gabas.

A cewar rahoton, ci gaban ya sa daruruwan abokan cinikin banki sun makale kuma ba sa iya gudanar da ayyukansu. Wasu daga cikin ma’aikatan bankunan sun ce ma’aikatan hukumar raya babban birnin Owerri ne suka rufe su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here