Gwamnatin Kaduna za ta Fara Amfani da Shafin Whatsapp Wajen Tattara Haraji

 

Hukumar tattara kudin haraji ta Jihar Kaduna za ta fara amfani da shafin WhatsApp, da kuma tsarin biyan kudi na kananan wayoyin hannu wato USSD wajen karbar haraji.

Shugaban hukumar Dr Zaid Abubakar wanda ya bayyana hakan jiya Laraba a wani taron tattaunawa kan tara haraji, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito ya ce za su yi hakan ne domin saukaka hanyar biyan harajin.

Dr Abubakar ya ce, amfani da kafar ta WhatsApp, wadda aka fi amfani da ita wajen sada zumunta da muhawara zai saukaka wa masu biyan haraji wahalar zuwa banki da sauran wuraren biyan haraji domin biya.

An shirya taron tattaunawar ne a tsakanin kungiyoyin kare fararen hula da wasu da suka jibanci haraji da mulki da hadin guiwar hukumar tattara haraji ta Jihar ta Kaduna da kuma kungiyar Christain Aid.

Ya bayyana cewa a tsarin za a bai wa duk wanda yake biyan haraji wata lamba ta musamman wadda zai rika amfani da ita wajen biyan ta wannan hanya.

Haka kuma ya ce za a yi amfani da tsarin aika kudi na USSD, wanda masu wayoyi kanana da ba a hada su da intanete suma za su iya biyan harajin cikin sauki da sauran abubuwa da suka danganci harajin.

Hukumar ta ce za ta bullo da wadannan tsare-tsare ne su fara aiki kafin karshen watan Maris da ke tafe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here