Jami’an Tsaro Sun Kama Gungun Miyagu a Jihar Anambra

 

Jami’an ƴan sanda sun kama wani gungun masu aikata miyagun laifuka a ƙaramar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra.

Ƴan sandan na rangadi ne tare da ƴan sintiri lokacin da suka gamu da miyagun riƙe da muggan makamai.

Tawagar jami’an tsaron sun bi gungun har sai da motar da miyagun ke ciki ta faɗa wani rami.

Bayanin hakan na cikin sanarwar da kakakin rundunar, DSP Tochukwu Ikenga ya fitar inda ta ƙara da cewa biyu daga cikin miyagun sun shiga hannu bayan musayar wutar da aka yi.

A cewar sanarwar, an gano bindigogi ƙirar AK47 guda huɗu da mota ƙirar Toyota SUV.

Rundunar ta kuma ce ta kama wata mota ƙirar Toyota Venza a ƙaramar hukumar Anaocha sai dai matuƙin motar ya tsere bayan da ya hangi jami’an tsaron.

Binciken da suka gudanar ya kai ga gano gidan harsasai cikin motar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar CP Aderemi Adeoye ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin inda kuma ya umarci tawagar ko-ta-kwana a yankin Awkuzu su gudanar da bincike kan lamarin.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here