Hukumar Zabe ta Jahar Kano Tayi Watsi da ‘Yan Takarar Kananan Hukumomi

Hukumar zabe ta jahar Kano KANSIEC tayi watsi da yan takara shida bayan sun gaza tsallake gwajin kwayoyi.

Prof Sheka, shugaban hukumar ya ce jamiyyun da yan takarar su ka fito na iya maye gurbin yan takarar cikin satin nan.

Wasu majiyoyi daga hukumar NDLEA sun bayyana cewa yan takara 20 ne shida kamar yadda KANSIEC tayi ikirari ba.

Gabanin zaben 16 ga Janairu na kananan hukumomin jahar Kano, hukumar zabe mai zaman kanta ta jahar (KANSIEC) a ranar Laraba ta ce tayi watsi da yan takara shida saboda sun kasa tsallake gwajin kwayoyi, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito KANSIEC ta ce da kirkiri gwajin kwayoyi kuma wajibi ne ga duk dan takarar da ke son neman kujerar shugaban karamar hukuma ko kansila a zabe me zuwa saboda yawaitar shaye shaye a jahar.

Shugaban hukumar, Prof Garba Ibrahim Sheka, wanda ya tabbatar da batun yayin da yake zantawa da Daily Trust akan shirye shiryen da hukumar ke yi na zaben, ya ce sun gano yan kwaya shida daga cikin yan takarar.

Ya ce, “bayan gwajin kwayoyin da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta gudanar ga duk yan takarar ciyamomi 44 da kansiloli 484, an tabbatar da shida daga ciki yan kwaya ne kuma mun cire su daga yan takara.

“Duk yan takarar shida kujerar kansila suke nema babu dan takarar ciyaman. “Jamiyyun su na iya amfani da wannan satin don gabatar da wasu yan takarar”, in ji Sheka.

Sheka ya bayyana cewa dokar zata zama izna ga matasa masu sha’awar siyasa da su guji shaye shaye.

Sai dai, wasu majiyoyi daga NDLEA sun bayyana cewa mutane 20 ne, ba shida kamar yadda KANSIEC tayi ikirari ba, aka tabbatar da yan kwaya ne kuma ciki har da yan jamiyyar APC mai mulkin jahar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here