Kasashen Afrika 7 da ‘Dan Najeriya Zai Iya Zuwa a Mota

 

Akwai wasu kasashe dake iyaka da Najeriya da mutum zai iya zuwa a mota don yawon bude ido ba tare da hawa jirgi ba.

Tafiya a mota na da amfani matuka saboda mutum zai iya ganewa idonsa abubuwa daban-daban tare da iya daukan hotuna sabanin jirgin sama.

Domin fita daga Najeriya da mota, ana bukatar mutum ya mallaki Fasfot, katin zama dan kasa, da kuma katin shaidan kayi rigakafin zazzabin Yellow Fever, sai kuma isasshen kudi.

Ga jerin wasu kasashen Afrika da dan Najeriya zai iya ziyarta a mota:

1. Kasar Ghana

Mutum zai iya bin shata idan suna da yawa ko kuma ya shiga motar haya daga Jibowu ko Maza-Maza a Legas zuwa birnin Accra ko Weija a Ghana.

Ka tabbatar ka yi tanadi kudin Ghana wato Cedis. 2. Kasar Togo Za ka iya zuwa Togo tare da motocin kamfani ko kuma ka shiga Bas a tashar Mile 2 a Legas.

3. Kasar Mali

Mutum zai iya bin shahrarriyar hanyar Katsina-Maradi duk da cewa akwai kalubale.

Hakazalika mutum zai iya zuwa Togo sannan ya shiga motar Mali.

4. Kasar Kamaru

Za ka iya shiga Kamaru ta kudancin Najeriya.

Da birnin Calabar a jahar Cross River, za ka je garin Ekon, sannan ka isa iyakar Kamaru. Za ka iya shiga motar Bas daga Ekom zuwa Douala.

5. Kasar Ivory Coast

Kasar Ivory Coast, ko Côte d’Ivoire na yammacin Afrika. Za ka iya zuwa Ivory Coast ta Maza-Maza a jahar Legas.

6. Kasar Benin

Za ka shiga mota a tashar Mile 2 a Legas zuwa Seme. Sannan ka shiga motar Tasi zuwa Kotono.

7. Kasar SierraLeone

Za ka iya shiga mota a tashar Mile 2 a Legas.

Hakazalika zaka iya shiga kwale-kwale, kamar yadda yan wasan Super Eagles suka yi kwanaki. A bangare guda, mun kawo muku jerin shugabannin kasashen Afrika mafi daukan Albashi.

A cewar Answer Afrca, shugaban kasar Kamaru, Paul Biya, ne shugaban kasa a Afrika mafi yawan albashi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here