Kiran Gwamna Masari ‘Dan Giya: Kungiyar Meyetti Allah Reshen Katsina ta ce ba ta da Alaka da Furuncin Alhassan

 

Miyetti Allah nisanta kan ta daga furucin sakatarenta, Saleh Alhassan da ya yi akan gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari, inda ya kira shi da dan giya kuma gajiyayyen shugaba.

Rahotanni sun nuna yadda gwamna Masari ya fito karara ya bayyana cewa yawancin ‘yan bindiga Fulani ne, wanda hakan ya hassala sakataren kungiyar har ya yi furucin akan sa.

A ranar Juma’a shugaban kungiyar na reshen jahar Katsina, Hassan Kuraye ya ce kungiyar ba ta da alaka da furucin Alhassan, sannan bai nemi izinin kungiyar ba kafin ayi hirar da yayi furucin ba.

Jahar Katsina – Kungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah ta nuna rashin amincewar ta da furucin da sakataren ta na kasa ya yi akan gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari inda ta kira shi da dan giya, Premium Times ta rawaito.

Rahotanni sun nuna yadda Masari ya bayyana yana cewa yawancin ‘yan bindiga Fulani ne, furucin da ya tunzura Alhassan har ya caccaki gwamnan.

Shugabannin kungiyar na reshen jahar Katsina sun nisanta kansu daga furucin Saleh Alhassan.

Kamar yadda Premium Times ta rawaito, Alhassan ya furta munanan kalaman ga gwamnan ne saboda haushin cewa da ya yi yawancin ‘yan bindiga Fulani ne.

Furucin da Masari ya yi har Saleh Alhassan ya kira shi da dan giya

A wata hira da aka yi da Gwamna Masari a Channels TV ya ce:

“Akwai mutane iri na da suke irin yare na har da irin addini na a cikin su,”

“Don haka anan akwai ‘yan bindiga; ba wasu halittu bane na daban, mutane ne da muka sani kuma sun dade su na rayuwa tare da mu tsawon shekaru 100 ma.”

Shugaban Miyetti Allah na jahar Katsina ya ce sakataren ba ra’ayin kungiyar ya fadi ba

Sai dai kamar yadda Premuim Times ta rawaito, a wata tattaunawa da manema labarai su ka yi da Hassan Kuraye, shugaban kungiyar na jahar Katsina, Alhassan ya fadi son ran sa ne kuma bai nemi izini ba kafin ayi hirar da shi

A cewarsa:

“Munyi magana da shugabannin kungiyar Miyetti Allah na kasa sun ce Alhassan bai bayyana matsayar kungiyar ba dangane da lamarin”

Yayin bayyana ra’ayin sa dangane da furucin Masari, Kuraye ya bayar da hakuri a madadin kungiyar ga Masari inda ya bukaci ya yafe musu kuma ya manta da maganganun da sakataren su ya yi akan sa.

Ya ce shugaban kungiyar zai tattaro sauran masu ruwa da tsakin kungiyar a mako mai zuwa don su yi magana da gwamna akan lamarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here