Kammala Wa’adi: Gwamnonin Najeriya 18 da Zasu Sauka Daga Kan Kujerarsu a 2023

 

A ka’idar siyasar Najeriya, shugaban kasa da gwamnoni kan yi shekaru takwas ne kacal a kan karagar mulki.

Duba ga wannan al’ada ta siyasar kasar, kimanin gwamnoni 18 masu ci a yanzu ne za su hakura da wannan kujera domin za su kammala wa’adinsu na biyu a 2023.

Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya so zarcewa a wa’adi na uku a lokacin mulkinsa amma mutane suka yi adawa da hakan.

Tarayyar Najeriya – Ga dukkan alamu akwai yarjejeniya a fagen siyasar Najeriya cewa babu wani shugaba ko gwamna da zai iya yin tazarce a karo na uku duk da cewar ba a fayyace wannan a cikin kundin tsarin mulkin kasar ba.

Wannan al’ada tayi aiki sosai ne a ƙarshen gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a 2007 lokacin da aka yi ikirarin cewa zai sake yin wani wa’adin (bayan ya shae shekaru takwas a karagar mulki) inda aka yi adawa da hakan kamar yadda yake a wallafar Vanguard.

Wannan na tabbatar da cewa yawancin gwamnoni masu ci a yanzu da suka riga suka hau kujerar mulki a karo na biyu ba za su iya shiga babban zaben da ake sa ran za a yi a 2023 ba.

Legit.ng ta kawo cikakken jerin sunayen irin wadannan gwamnoni:

1. Gwamna Okezie Ikpeazu (Abia)

2. Gwamna Udom Gabriel Emmannuel (Akwa Ibom)

3. Gwamna Willie Obiano (Anambra)

4. Gwamna Samuel Ortom (Benue)

5. Gwamna Benedict Ayade (Cross River)

6. Gwamna Ifeanyi Okowa (Delta)

7. Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu)

8. Gwamna Badaru Abubakar (Jigawa)

9. Gwamna Abdullahi Ganduje (Kano)

10. Gwamna Aminu Masari (Katsina)

11. Gwamna Abubakar Atiku Bagudu (Kebbi)

12. Gwamna Abubakar Sani Bello (Neja)

13. Gwamna Simon Lalong (Filato)

14. Gwamna Nyesom Wike (Ribas)

15. Gwamna Aminu Waziri Tambuwal (Sokoto)

16. Gwamna Darius Ishaku (Taraba)

17. Gwamna Dave Umahi (Ebonyi)

18. Gwamna Nasir El-Rufai (Kaduna)

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here