2023: Sam Ban Shirya Zuwa Villa Domin na Mike Kafa na Sharbi Jar Miya ba – Tinubu

 

Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana abin da ya shirya yiwa ‘yan Najeriya, da kuma irin kiran da ya amsa.

‘Yan takarar shugaban kasa a Najeriya na ci gaba da tallata manufofinsu na gaje Buhari a zaben 2023 mai zuwa.

Tinubu ya gana da wasu jiga-jigan siyasar Najeriya a birnin Landan, inda suka tattauna makomar siyasa.

Najeriya – Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kadan daga alherin da ya tanadarwa ‘yan Najeriya idan ya gaji Buhari.

Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya ce sam bai shirya zuwa Villa domin ya mike kafa ya sharbi jar miya ba, zai zo ne dan yiwa ‘yan Najeriya aikin da ya cancanta.

A wani sako da ya yada a shafinsa na Twitter, Tinubu ya bayyana, cewa an kira shi ya tsaya takara ne saboda kaunar da yake yiwa kasar nan da kuma ayyukan da ya sa a gaba gareta.

A cewarsa:

“Ba mu zo nan don shan romo ba. Mun zo ne don yin abin da ya dace ga mutane da kasarmu.

“Mun zo nan ne don amsa wata kira mai girma, mai girma ainun. Wannar kiran dai itace kaunar Najeriya. Ba mu kuskura mun yi wasa da wannan damar ba saboda ba lallai mu iya samun wata ba.”

Wannan kalami na dan takarar shugaban kasa a APC na zuwa ne jim kadan bayan dawowarsa daga Landan, inda ya gana da wasu jiga-jigan siyasar Najeriya.

Sakamakon ganawar Tinubu da ‘yan siyasar Najeriya a Landan bai zama batun siyasa zalla ba, an tattauna kan abubuwan da suka shafi makomar Najeriya, inji gwamnan Ribas Nyesom Wike.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here