Kotun Tarayya ta Sake Hana Bayar da Belin Abba Kyari

 

FCT, Abuja – Babbar kotun tarayya dake zama a Abuja ta saka ranakun 19, 20 da 21 na watan Oktoban shekarar nan domin shari’ar dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sandan Najeriya, Abba Kyari da wasu mutum hudu.

Mai shari’a Emeka Nwite ya saka ranakun a hukuncin da ya yanke na ranar Talata a babban birnin tarayyar kasar, Channels TV ta rahoto.

Hakazalika, ya yi watsi da bukatar bada belin dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da wasu mutum hudu.

Hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi ta NDLEA ce ta gurfanar da su kan zargin safarar hodar iblis.

An gurfanar da Kyari tare da wasu dakatattun jami’an ‘yan sanda da suma hada da ACP Sunday Ubia, ASP James, Sifeta Sunday Agirigba da Sifeta John Nuhu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here