Alkalin Alkalan Najeriya ya Nada Alkalan da za su Saurari Korafe-Korafen Zabukan 2023

 

Alkalin alkalan Najeriya mai shari’a Olukayode Ariwoola ya rantsar da alkalan da za su jagoranci sauraron korafe-korafen zabukan kasar na 2023

An yi bikin rantsar da alkalan ne ranar Litinin a harabar hukumar da ke kula da harkokin shari’a ta kasar a Abuja babban birnin kasar

Yayin da yake nada alkalan babban alkalin alkalan kasar ya umarce su, da su dauki aikinsu da matukar muhimmanci, yana mai gargadinsu da cewa ba zai lamunci wasa da aiki ba.

Daga cikin wadanda suka halarci taron har da shugabar kotun daukaka kara ta kasar mai shari’a Monica Dongban-Mensem, da shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Mahmood Yakubu, da kuma sauran alkalan kotun daukaka kara ta kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here