Yanzu Haka Najeriya na da Lita 1.9bn na Man Fetur a Ajiye – Mista Timipre Sylva

Yanzu haka Najeriya tana da lita biliyan 1.9 na man fetur a cewar karamin ministan albarkatun man fetur na Najeriya, Mista Timipre Sylva.

Ministan ya yi ikirarin cewa lita biliyan 1.9 na man fetur na iya gamzar da kasar na tsawon kwanaki 32.

Sylva ya bayyana haka ne a Abuja yayin da yake magana a gaban majalisar zartarwa ta tarayya a zaman da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Timipre Sylva, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur ya bayyana cewa yanzu haka Najeriya na da lita biliyan 1.9 na man fetur a ajiye.

A cewarsa, wannan mai na iya gamsar da bukatun kasar na tsawon kwanaki 32, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ministan ya bayyana haka ne jiya Laraba 9 ga watan Maris a Abuja yayin da yake magana a gaban majalisar zartarwa ta tarayya a zaman da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Babban Manajin Darakta na Kamfanin Mai na Najeriya Mista Mele Kyari ya raka shi a taron na FEC da aka yi.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa, ofishin mataimakin shugaban kasa, Mista Laolu Akande ne ya bayyana haka bayan taron.

Vanguard ta Akande yana cewa:

“Akwai lodin sa’o’i 24 da ke gudana a dukkan gidajen man da ke aiki tare da Hukumar Ma’aikatar Jiha da kuma Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya don tabbatar da cewa lamarin ya daidaita yadda ya kamata.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here