Oshiomhole ya Koka Kan Siyan Litar Man Fetur a N1,000
Tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya koka kan siyan litar man fetur a N1,000.
Oshiomhole ya koka cewa duk da kashe fiye da naira tiriliyan kan tallafin mai, yan Najeriya na biyan fiye da farashin kasuwa.
A cewar Oshiomhole, N7trn kan tallafin mai bai kunshi kudaden ci gaban fetur ba, yana mai cewa dole a rike wani kan haka.
Adams Oshiomhole, tsohon shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, ya koka kan tsadar farashin man fetur a Najeriya.
Da yake jawabi a shirin Politics Today na Channels TV, tsohon gwamnan na jihar Edo, ya koka cewa ya siya litar mai kan N1,000.
Akwai mai hannu a karancin man fetur Oshiomhole
Read Also:
Oshiomhole ya ce lamarin ba abun dariya bane, yana mai cewa wani na da hannu a karancin man fetur a kasar nan.
Ya ce a yanzu haka, kasar na kashe kimanin naira tiriliyan 7 kan tallafin man fetur amma abun takaici shine cewa yawancin yan Najeriya na biyan fiye da farashin da ya kamata a siyar da mai a kasuwa.
Tsohon Shugaban kungiyar kwadago na kasar ya bayyana cewa duk da naira tiriliyan 7 na tallafin mai, akwai kuma wani kudin haraji na fetur, yana mai jaddada matsayinsa na farko cewa wasu ne ke da hannu a lamarin.
A cewarsa, idan yan Najeriya suna ganin ba sabon abu bane cewa mun saba samun karancin man fetur hatta a mulkin soja har zuwa Shugaba Olusegun Obasanjo, Yar’adua da Jonathan, ana iya cewa karancin mai ya zama dadaddiyar matsala amma wannan baya nufin abun yarda ne.
Tun a Janairu 2022 me kasar ke fama da matsalar karancin man fetur da tsadar farashi a yankuna daban-daban na kasar.