Jam’iyyar PDP ta Nemi Kotu da ta Tsige Gwamna Buni Daga Kan Kujerarsa

 

Jam’iyyar PDP ta maka gwamna Buni a kotu bisa zarginsa da saba ka’idar tsarin mulkin Najeriya.

PDP ta bukaci kotu da ta tsige gwamnan, kuma ta gaggauta maye gurbinsa da ‘yan takarar PDP da suka fadi a zaben 2019.

PDP ta ce bai kamata gwamnan ya rike matsayin shugaban jam’iyya na riko da kuma kasancewarsa gwamna.

Jam’iyyar PDP ta fara daukar matakin doka na tsige gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni daga mukaminsa bisa zargin sabawa kundin tsarin mulki da ya hana shugaba gudanar da ofisoshi biyu a lokaci daya, THISDAY ta ruwaito.

PDP a cikin karar da aka shigar ranar 12 ga watan Agusta, tana zargin Buni ya sabawa sashi na 183 na kundin tsarin mulki saboda a matsayin gwamna ya yarda ya zama Shugaban Kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC.

Wadanda suka shigar da karar sun hada da Umar Damagum da Baba Aji a ta hanyar Emeka Etiaba (SAN), sun dage cewa Buni ya zama ba gwamna ba daga lokacin da ya yarda ya karbi matsayin Shugaban Kwamitin rikon kwarya na APC.

Don haka masu shigar da karar sun nemi kotun da ta umarci babban alkalin jahar Yobe ko wani babban mutum da ke kusa da babban alkalin da ya gaggauta rantsar da Damagum da Aji a matsayin Gwamna da Mataimakin Gwamnan Jahar Yobe.

PDP ta bayyana haka ne saboda Damagum da Aji su ne ‘yan takarar jam’iyyar PDP suka zo na biyu a zaben gwamna na 2019.

Ta ina maganar ta samo asali?

Wannan batu ya zo ne a cikin damuwar da ta taso bayan hukuncin babbar kotun, wacce ta tabbatar da nasarar Rotimi Akeredolu a matsayin gwamnan jahar Ondo, in ji The Cable.

A cikin hukuncin 4:3 wanda ya tabbatar da Akeredolu a matsayin gwamnan Ondo, kotun koli ta tado da magana kan cancantar Buni na gudanar da babban taron APC da tsayar da ‘yan takara.

Da yake tsokaci game da batun, Festus Keyamo, karamin ministan kwadago, ya ce domin jam’iyyar ta guji rikicin kotu, ya kamata APC ta dakatar da babban taron ta kuma maye gurbin Buni.

Amma jam’iyyar ta yi watsi da maganarsa. Magnus Abe, tsohon sanata kuma mamba a hukumar kamfanin mai na kasa (NNPC), da Ovie Omo-Agege, mataimakin shugaban majalisar dattijai, suma ba su yarda da matsayar Keyamo ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here