Kashi 80 Cikin 100 na Mutanen Afirka ba a yi Musu Allurar Rigakafin Corona ba – Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce kashi 80 cikin 100 na mutanen Afirka har yanzu ba a yi musu allurar riga-kafin corona ko da ɗaya ba.
Dr Tedros ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro ta intanet yayin cika shekara daya da kaddamar da shirin samar da rigakafin a duniya da ake kira Covax.
Read Also:
Ya ce “kiyasinmu ya nuna cewa riga-kafin da za a samar za ta isa a yi wa dukkanin manya na duniya kuma har a kara yi wa mutanen da ke cikin hadarin kamuwa da cutar sosai zuwa wata uku na farkon shekaran nan”.
Covax shiri ne na tabbatar da raba daidai a tsakanin kasashen duniya wajen samar da riga-kafin corona.
Shugaban na WHO ya ce shirin ya gamu da nakasu sosai saboda abin da ya kira “kaka-gida” da kasashe suka yi a kan rigakafin da kuma yadda kamfanonin da ke samar da ita suka fi bayar da fifiko ga kasashe masu karfin arziki.