Roma ta Dauki Lukaku Daga Chelsea

 

Dan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku ya amince ya koma Roma ta Italiya a matsayin aro na tsawon kakar wasa daya daga Chelsea.

Dan wasan mai shekaru 30 ya koma Seria A bayan da ya shafe kakar wasa ta bara a matsayin aro tare da Inter Milan, wanda ya taimaka mata kai wa wasan karshe na gasar zakarun Turai.

An ruwaito cewa ya ki amincewa da kudirin komawa wata kungiyar da ke buga Saudi Pro League.

An rawaito cewa Lukaku ya amince da rage albashinsa domin ya sake haduwa da kocinsa Jose Mourinho a Roma.

Mourinho ya jagoranci Lukaku na takaitaccen lokaci a shekarar 2013-14, lokacin da dan wasan ya fara zama a Chelsea, kafin kocin ya dauko shi zuwa Manchester United daga Everton a 2017 a kan fam miliyan 75.

Bayan ya koma Inter kan kwantiragin dindindin daga United a shekarar 2019 kan fam miliyan 74, Lukaku ya koma Chelsea a kan fam miliyan 97.5 a shekarar 2021 amma komawarsa bai yi nasara ba kuma tun watan Mayun 2022 bai buga wa Chelsea wasa ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com