Kifewar Kwale-Kwale: Mutane 6 Sun ɓace a Jihar Neja

 

Aƙalla fiye da fasinjoji shida ne aka bayyana cewa sun ɓace bayan da wani kwale-kwale ya kife da su a kogin Zamre a ƙaramar hukumar mulki ta Agwara da ke jahar Neja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru a ranar Litinin lokacin da matafiyan waɗanda galibinsu manoma ne ke kan hanyar tafiya daga Neja zuwa jahar Kebbi.

A halin yanzu an gano gawar mutum ɗaya daga cikin su, sannan ana ci gaba da neman sauran da suka ɓacen.

Rahotan ya ce kwale-kwalen na ɗauke da fasinjoji 20 da suka haɗa da mata da ƙananan yara, inda ya kife sakamakon tsayawar injin daidai lokacin suka kai tsakiyar kogin.

Jaridar ta ruwaito cewa Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jahar Naija ta tabbatar da aukuwar lamarin sai dai babban daraktanta, Garba Salihu, ya ce kawo yanzu ba a kai ga samun cikakkun alƙalumman waɗanda suka mutu ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com